19 Mayu 2021 - 14:04
Pogba Da Diallo Sun Daga Tutar Falastinu Bayan Gama Wasan Manchester United Da Fulham

'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta manchester United Paul Pogba da Ahmad Dillo sun daga tutar Falastinu , bayan kammala wasan da kungiyar ta buga tare da Fulham.

ABNA24 : Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewa, ba za a ci 'yan wasan biyu wata tara ba, domin kuwa ba laifi ba ne don wani dan wasa ya daga tutar Isra'ila ko ta Falastinu a filin kwallo.<p "="">Baya ga haka kuma Ole Gunnar Solskjaer ya kara da cewa, dole ne a girmama ra'ayin 'yan wasan biyu.

342/